Bangaren kasa da kasa; a karo na goma sha biyu a fara wani taron karawa juna sani na kasa da kasa kan ayyukan Hajji da yadda za a inganta da kuma kawo sauki ga maniyata da kuma tunanin hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a lokacin aikin Hajji kuma an fara wannan taro ne a ranar shida ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jami'ar Ummul Kur'a da ke birnin na makka.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karo na goma sha biyu a fara wani taron karawa juna sani na kasa da kasa kan ayyukan Hajji da yadda za a inganta da kuma kawo sauki ga maniyata da kuma tunanin hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a lokacin aikin Hajji kuma an fara wannan taro ne a ranar shida ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jami'ar Ummul Kur'a da ke birnin na makka.Bayan an nakalto daga jaridar Ukkaz da ake buga ta a kasar ta Saudiya cewa; wannan taro ana gudanar das hi ne karkashin sanya idon Khalid Alfaisal amirin yankin birnin Makka tare da halartar masana da kwararru da masu bincike da nazari a lamuran da suka shafi ayyukan hajji da umara kuma wadannnan masana da kwararru da suka halarci wannan taro sun fito ne da kasar ta Saudiya da kuma sauran kasashen duniya musamman kasashen musulmi da duk shekara dubbu ko miliyoyi ke tafiya kasar ta Saudiya domin sabe farali daga cikin shikashikai biyar na addinin musulunci.
1017397