IQNA

An Kafa Kwamitin Kula Da Tarukan Mata Na Fadakar Musulmin Duniya

20:41 - May 28, 2012
Lambar Labari: 2336340
Bangaren kasa da kasa, an kafa wani kwamiti a babbar cibiyar kula da harkokin ahlul bait ta duniya na mata da zai kula da tarukansu kan fadakar musulmin duniya da kuma abubuwan da suke faruwa yanzu a yankin gabas ta tsakiya da sauran kasashen musulmi inda turawa suke jagorantar boren jama’a domin kifar da gwamnatoci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic awakening cewa an kafa wani kwamiti a babbar cibiyar kula da harkokin ahlul bait ta duniya na mata da zai kula da tarukansu kan fadakar musulmin duniya da kuma abubuwan da suke faruwa yanzu a yankin gabas ta tsakiya da sauran kasashen musulmi inda turawa suke jagorantar boren jama’a domin kifar da gwamnatoci da ba su shiri da su karnukan farautarsu da ke yankin.
A wani labarin kuma jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kirayi ‘yan majalisar kasar da su yi dukkanin abin da za su iya wajen sauke nauyi na Ubangiji da kuma na al'umma da ke wuyansu yana mai kiransu da su yi watsi da soyace-soyacen zukatansu don su sami damar yi wa al'ummar da suka zabe su aiki.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya aike wajen bikin kama aikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran karo na tara da aka gudanar a cikin majalisar.
Jagoran ya ce bude majalisar a yau wani sako ne na al'ummar Iran zuwa ga duniya baki daya dangane da irin kuduri da aniyar da suke da ita na ci gaba da tafarkin da suka rika duk kuwa da makirce-makircen da makiya suke kulla musu ba don komai ba sai don saboda kafa tsari na musulunci da suka yi a kasarsu.
A safiyar yau ne dai aka gudanar da bikin fara aikin majalisar shawarar musulunci ta kasar Iran karo na tara inda ‘yan majalisar suka yi rantsuwar kama aiki da kuma yin alkawarin yin aiki da hidima wa al'umma da kuma kare mutumcin kasar Iran.
1017733

captcha