Bangaren kasa da kasa: hukumar afuwa ta duniya a ranar takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ta mikawa mahukumtan kasar Saudiya wani rahoto da a ciki ta bukaci sakin fitattun yan shi'ar kasar da ta kamai kuma take ci gaba da tsare das u ba tare da wani zargi da yi masu adalci ba.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hukumar afuwa ta duniya a ranar takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ta mikawa mahukumtan kasar Saudiya wani rahoto da a ciki ta bukaci sakin fitattun yan shi'ar kasar da ta kamai kuma take ci gaba da tsare das u ba tare da wani zargi da yi masu adalci ba.Bayan an nakalto daga majiyar labarai ta Arabic .rt cewa; wannan hukumar ta bukacin shugabannin da masu fada a ji a kasar saudiya das u gaggauta sakin yan shi'ar da suke tsare das u saboda kawai sun gudanar da wata zanga zanga ta lumana a yankin Alsharkiya yankin da yawancin yan shi'a ke zaune a kasar ta Saudiya kuma har ula yau ta bukaci sakin duk wanda aka kama da ci gaba da tsare shi ba tare da ana zarginsa da wani laifi ba . a cikin wannan rahoto mai sunan kokarin toshe bakin daruruwan masu nuna adawa a yankin Sharkiya an kama daruruwan yara kanana yan makaranta daga watan maris din day a gabata a wannan kasa ta saudiya duka karkashin manufa da zaluncin mahukumtan saudiya da kuma hanyar da suke bi na hana fitowa zanga zangar nuna adawa da salon mulkinsu na take sauran kabilu da mabiya mazhabobi ko bayyana ra'ayin day a sabawa mahukumtan kasar.
1018489