Bangaren nazari da ilimi: malaman addini a kasar Indiya a ranar litinin takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani zama da suka yi a garin Jugipura Najib Abad da ke lardin Otarpardesh na kasar Indiya sun jaddada cewa amerika har abada ba za ta taba gurbatawa musulmi akidarsu ba .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: malaman addini a kasar Indiya a ranar litinin takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani zama da suka yi a garin Jugipura Najib Abad da ke lardin Otarpardesh na kasar Indiya sun jaddada cewa amerika har abada ba za ta taba gurbatawa musulmi akidarsu ba.Malaman sun gudanar da wannan taron karawa juna sani domin isar da sako da kuma tunkarar makircin kasar amerika a daidai wannan lokaci da take kokarin gurbata akidar musulmi da sunan musulmi da addininsu a idanun sauran al'ummomin duniya da kuma danganta duk wani abu na ta'addanci da musulmi alhali kuwa addinin musulunci addini ne day a yi fice wajan yaki da duk wani abu ko lamari da ked a dangantaka da ta'addanci.
1016760