Bangaren kasa da kasa: an samu da Karin mutane a tsakanin kasashen yammacin Turai da ke kokowar ganin an haramta shigar kayan da ke fitowa daga Haramtacciyar kasar isra'ila musamman kasar Britaniya aka fi samin masu gabatar da wannan bukata kamar yadda kasashen Iskandariya da Afrika ta kudu suka dauki irin wannan mataki kuma tuni gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta nuna damuwa matuka da wannan matsala.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an samu da Karin mutane a tsakanin kasashen yammacin Turai da ke kokowar ganin an haramta shigar kayan da ke fitowa daga Haramtacciyar kasar isra'ila musamman kasar Britaniya aka fi samin masu gabatar da wannan bukata kamar yadda kasashen Iskandariya da Afrika ta kudu suka dauki irin wannan mataki kuma tuni gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta nuna damuwa matuka da wannan matsala. Tuni al'ummomi da kungiyoyi da hukumomi suka fara bayyana ra'ayinsu da kuma kara himma ta ganin an cimma burin da aka sanya a gaba na yaki da fito na fito da Haramtacciyar kasar Isra'ila da taka mata birki kan zaluncin da take nunawa al'ummar Palasdinu da kuma babakeren da ta ke yi dokokin kasa da kasa da suka tanadi kare hakkoki da dokokin na kasa da kasa.
1018551