Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine cewa, dubban mutanen yankin birnin Qods ne suka gudanar da wani gangami domin nuna rashin amincewarsu da hankoron yahudawan sahyuniya na mayar da yankin mallakinsu tare da mayar da palastinawa saniyar ware acikin harkokin yankin baki daya.
A wani bangare jaridar ta kawo labarin da ke cewa, jaridardar Lefigaro ta kasar faransa ta buga wani rahoton sirri da ke cewa, gwamnatin kasar Qatar ta tura mayakan alkaida tsakanin 300 zuwa 400 zuwa cikin Syria domin kaddamar da hare-hare.
Jaridar ta ce Qatar tana daukar nauyin ‘yan alkada da suka fito daga kasashen larabawa daban-daban domin tura Syria, wasu sukan shiga kasar ta iyakokinta da Turkiya, wasu kuma ta iyakokin kasar da Jordan ko Lebanon, rahoton ya ce masarautar Qatar tana daukar nauyin iyalan duk wani dan alkaida da aka kashe a Syria ko kuma wajen kai harin kunar bakin wake da bama-bamai.
Gidan talabijin Syria ya nuna wasu daga cikin ‘yan ta’adda da aka kama a garin Homs da suke yaki tare da ‘yan tawayen Syria, wadanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen larabawa daban-daban musamman daga Libya, Tunisia, Masar, Saudiyya, Kuwait da Lebanon, gami da wasu ‘yan kasar kasar Pakistan. 1019486