IQNA

Za A Gudanar Da Mataki Na Karshe Na Gasar Karatun Kur’ani A jami’ar Mostafa (SAW)

17:14 - May 31, 2012
Lambar Labari: 2338349
Bangaren kur’ani, ana shirin fara gasar kur’ani a mataki na karshe na jami’ar Mostafa (SAW) tare da halartar wakilin jagoran juyin juya halin muslunci bababr cibiyar kula da harkokin wadanda suka shada da sadaukantarwa a lokacin da kasar ta yi fama da yaki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo cewa ana shirin fara gasar kur’ani a mataki na karshe na jami’ar Mostafa (SAW) tare da halartar wakilin jagoran juyin juya halin muslunci bababr cibiyar kula da harkokin wadanda suka shada da sadaukantarwa a lokacin da kasar ta yi fama da yaki wanda ak akallafa mata tsawon shekaru takwas.
A bangare guda kuma fitaccen malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu da kuma muggan sarakuna da suke mulkar al’umma bisa tsari na zalunci da danniya.
Malamin ya bayyana hakan a wagaban wani babban taro da aka kira na tunawa da ranar shahadar Imam bakir Sadr a birnin Najaf mai alfarma, wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na duniyar musulmi da ma kasashen Asia da dama, gami da manyan malaman addini da na jami’oi na kasar Iraki, inda ya bayyana siffofinsa da cewa mutum ne da ya sadaukantar da ransa saboda Allah da kuma daukakar addinin Allah.
malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr baya ga cewa shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu, shi ne kuma mutumin da ya kalubaanci zalunci dawagitan Iraki ba tare da wani shayi ba.
1020626

captcha