IQNA

Zaman Taron Kasashen Musulmi Na Yankin Gabas Ta Tsakiya A Birnin Moscow

17:12 - May 31, 2012
Lambar Labari: 2338351
Bnagaren siyasa da zamantakewa, a cikin wannan watan ne za a gudanar da wani zaman taro kan harkokin tafiyarwa abirnin Moscow na kasashen musulmi da ke yankin gabas ta tsakiya wadanda akasarinsu mabiya tafarkin addinin muslunci ne.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a nahiyar Asia cewa a cikin wannan watan ne za a gudanar da wani zaman taro kan harkokin tafiyarwa abirnin Moscow na kasashen musulmi da ke yankin gabas ta tsakiya wadanda akasarinsu mabiya tafarkin addinin muslunci ne kuma larabawa.
Gungun lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin fararen hula.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da wakilai daga kasashen Iran, Yeman, Saudiyya, Lebanon, Morocco, Tunisia, Turkiya, Aljeria, Libya, Oman da kuma Qatar, wadanda dukakninsu mambobi ne akungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, wadda ta take wakiltar musulmi a taruka na kasa da kasa.
Kungiyar lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin mutane, duk kuwa d cewa ra’ayoyi kan boren larabawa sun sha banban.
1019633

captcha