IQNA

Jami’ar Azhar Za Ta Fara Gudanar Shirin Karatu Ta Hanyar Yanar Gizo

17:13 - May 31, 2012
Lambar Labari: 2338353
Bangaren kasa da kasa, babbar jami’ar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar za ta fara aiwatar da wani shiri na bayar da dama ga mutane da suke bukatar yin karatu a wannan jami’a daga nesa su yi amfani da hanyar yanar gizo domin yin karatun.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram cewa, jami’ar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar za ta fara aiwatar da wani shiri na bayar da dama ga mutane da suke bukatar yin karatu a wannan jami’a daga nesa su yi amfani da hanyar yanar gizo domin yin karatun kamar dai yadda wasu jami’oin suke yi.
A wani bayanin kuma ana shirin gudanar da zaben shugfaban kasar Masar zagaye na biyu tsakanin ‘yantakara biyu na kungiyar Ikhwanul muslimin da kuma Muhammad marsi da kuma mai zaman kansa kuma tsohon pira minista alokacin mulkin kama karya na Husni Mubarak Ahmad Shafiq wadanda dukakninsu suka samu kuri’u fiye da na sauran a zagayen farko.
Masu zabe sun fito a rana ta biyu don zaben shugaban kasa a kasar Masar a yau Alhamis. Duk da cewa wasu suna ganin fitowar masu zaben shugaban kasa a jiya laraba bai kai na zaben yan majalisar dokokin kasar ba. Amma duk da haka fitowar tana da yawa har sai da wasu suka kasa kada kuri'arsu a jiya don yawan masu zabe, don haka ne suka fito a yau don kada kuri'arsu.
Babu wanin tashin hankali da ya faru a zaben a jiya dai, inda banda duwatsu da takalma da aka jefa kan dan takarar shugabancin kasa kuma tsohon Priminister a lokacin Mubarak wato Ahmad Shafiq, a lokacin da ya je rumfan zabe don kada kuri'arsa.
Kungiyar Ikhwanul muslimin dai ta bada sanarwan cewa dan takararta Muhammad Mursi, shi ne a gaba, hakama masu goyon bayan Amru Musa sun bayyan cewa dan takarar ikhwanul muslimin ne a gaba sannan dan takaransu Amru Musa yana biye da shi.
Idan babu dantakaran da ya sami fiye da kashi hamsin cikin dari daga cikin kuri'in da aka kada dai to sai an je zagaye na biyu a ranakun 16 da 17 na watan yuli mai zuwa tsakanin yan takararn da suka fi samun kuria.
1020228

captcha