IQNA

Taro Kan Kur’ani Da Ahlul Bait (AS) Da Matsayinsu A Cikin Al’umma

Bangaren fikira da ilimi, za a gudanar da wani zaman taro kan matsayin kur’ani mai tsarki da kuma limaman iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kasar Pakistan wanda zai gudana agarin Binjaba da ke kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan matsayin kur’ani mai tsarki da kuma limaman iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kasar Pakistan wanda zai gudana agarin Binjaba da ke kasar, kamar yadda aka saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci.
Ana sake gina wa mabiyar tafarkin iyalan gidan manzon Allah masallatansu da ‘yan ta’adda suka rusa a yankuna daban-daban na kasar Pakistan wanda ciyar Amal ta kasar da kuma cibiyar Imam Hussain ta kasar Kuwait suka dauki nauyin ginawa a yankuna uku na kasar da suka hada Benjab.
An bayar da lasisi ga kungiyoyin addinin muslunci kimanin arba’in da bakwai 47 domin gudanar da ayyuaknsu cikin izini a kasar Tajikistan kamar dai yadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar.
A karon farko ana shirin gudanar da wani shiri da aka kira da yunkurin nuna goyon baya ga masallacin Qods ta hanayar sadarwa wanda hakan shi ne karon farko da masana a wannan bangaren za su gudanar da irin wannan shiri a mataki na kasa da kasa.
1021937