IQNA

Zaman Taron Tunawa Da Marigayi Imam Khomeni (RA) A Birnin Paris

17:34 - June 04, 2012
Lambar Labari: 2339914
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da marigayi Imam Khomeni (RA) a dukaknin kasashen musulmi musamman a jamhuriyar musulunci ta Ira a can birnin paris ma na kasar Faransa musulmi da dama sun halraci zaman taron da aka gudanar domin tunawa da shi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da marigayi Imam Khomeni (RA) a dukaknin kasashen musulmi musamman a jamhuriyar musulunci ta Ira a can birnin paris ma na kasar Faransa musulmi da dama sun halraci zaman taron da aka gudanar domin tunawa da shi da kuma irin gwagwarmayar da ya yi da makiya musulunci na duniya baki daya.
A nasa bangaren jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran. Jagoran ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
A mahangar jagoran juyyin juyya halin musulumci, fucewar daukacin sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki na daga cikin manyan abubuwa masu mahimmanci da suka ja hankali kuma wanda aka yi galaba kansu, da suka biyo bayan namijin kokari da kishin kasar da jama'ar kasar Iraki suka nuna, Sannan, karbar bakoncin taron kungiyar hadin kan larabawa da kasar ta Iraki ta yi ya kara nuna karfin gwamnatin kasar. Ayatullah Ali Khamenei, ya kara da cewa, Wasu bangarori sun yi ta kokarin nuna cewa kasar Iraki, ba ta da wani matsayi a cikin kasashen larabawa, amma bayan taron kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudana a Bagdada, kasar Iraki, a yanzu na kan gaba a cikin wannan kungiyar, kuma praministan kasar ke jagorantar ta.

1021826
captcha