Bangaren al’adu da fasaha, za a gudanar da wani zaman taro dangane da rubutun da Imam Khomeni ya yi a lokacin rayuwarsa da kuma abubuwan da kunshe a cikin wadannan littafai nasa taron da zai samu halartar masana da malan addini da kuma wakilan cibiyoyin musulunci na kasar Faransa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka ana shirin gudanar da wani zaman taro dangane da rubutun da Imam Khomeni ya yi a lokacin rayuwarsa da kuma abubuwan da kunshe a cikin wadannan littafai nasa taron da zai samu halartar masana da malan addini da kuma wakilan cibiyoyin musulunci na kasar Faransa wanda zai gudana a babbar cibiyar musulmin birnin Paris.
Wani bayanin kuma ya yi nuni da cewa an gudanar da wani zaman taro a birnin Pretown na kasar saliyo da nufin tunawa da marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran tare da yin gwagwarmaya da makiya muslunci da all’ummar musulmi, kama daga sarki Shah har zuwa babban shaidan da kuma haramtacciyar kasar yahudawa.
Bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni da muke cikinsa.
A yayin wannan taro za a gabatar da jawabai wanda malamai da kuma masana gami da malaman jami’oi da maruta za su gabatar, inda za a yi bayani kan matsayinsa na ilimi da kuma irin gwagwarmayar da ya yi da manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, wadanda suke danne sauran al’ummomin duniya tare da dora manufofin siyasarsu kan duniya bisa zalunci.
1022290