Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sortaliraq cewa, ana ci gaba da ajiye wasu litatfai na addinin muslunci da aka rubuta su da hannu tun tsawon shekaru daruruwa da suka gabata a birnin Najaf Ashraf da ke kasar Iraki wadanda dukkaninsu suna cikin bababr cibiyar nan ta adana kayan tarihi ta Imam Ali (AS) da ke cikin birnin mai alfarma.
Yanzu haka an fara gudanar da shiirin bayar da horo kan karatu da hardar kur’ani mai tsarki a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma tare da halartar malan addini da kuma kwarrau kan harkokin koyarwa kamar dai yadda aka saba gudanarwa a kowaces hekara a wannan hubbafe mai tsarki.
Ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka kuma suke amfani da wannan damar domin cin zarafin musulmi a cikin kasar da ma wajenta.
Baynain ya ce dole kowa ya girmama addinin kowane bangare a cikin dokokin kasar Tunisia, musulmi ba shi da hakkin ya ci zarafin wani saboda shi ba musulmi ba ne, kamar yadda wani wanda ba musulmi ba ba shi da ahhaki ko hurumin cin zarafin muslmi, haka nan kuma ko da musulmin ne ba shi da hakkin ya yi kalaman batunci kan akidar musulmci saboda wasu ra’yoyi nasa, yin hakan ya saba ma kundin tsarin mulki.
1020513