Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Rashid Alganushi shugaban jam'iyar musulunci ta Alnahda a kasar Tunusiya a cikin wani jawabi day a gabatar ya bayyana cewa: ko shakka babu burinsu na samar da a'umma mai tafiya da zamani dole ta kasance karkashin tsarin musulunci.An nakalto daga majiyar labarai ta businessnews cewa; shugaban jam'iyar ta nahada islami a kasar tunusiya a daidai lokacin day a ke bayani kan juyin juya halin musulunci a kasar da bude hanyar kai wag a kafa gwamnatin al'umma a kasar ya bayyana cewa: juyin juya halin musulunci wata hanya ce da al'ummar kasar ta zaba da kuma kafa gwamnati mai la'akarin da raayin yawancin al'ummar kasar ta hanyar la'akarin da koyarwa da dokokin addinin musulunci kuma jam'iyarsu ta Alnahda islami tabbas za ta yi aiki da wannan tsari ta hanyar la'akari da hakkokin al'ummar kasar da kuma koyowar addinin musulunci.
1023101