Bangaren kasa da kasa; kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa take bayyana cewa: Ta yin Allah wadai da babbar murya kan harin ta'addanci da bom da aka kai wa cibiyar addini ta mazhabar shi'a a kasar Iraki da hakan ya yi sanadiyar shahadar gomomin fararen hula da kuma jikkata wasu fararen hulan dari da tis'in .
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa take bayyana cewa: Ta yin Allah wadai da babbar murya kan harin ta'addanci da bom da aka kai wa cibiyar addini ta mazhabar shi'a a kasar Iraki da hakan ya yi sanadiyar shahadar gomomin fararen hula da kuma jikkata wasu fararen hulan dari da tis'in .An nakalto daga gidan talbijin din Almanar cewa; kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar ta Labanon ta nuna alhininta da takaicinta da yadda aka kai wannan hari na rashin tausayi da kuma rashin imani kara kan fararen hula wadanda bas u san hawa balanta sabka bad a kuma yi masu kisan gilla a fili. Kuma ta yi kira da babbar murya kan mahukumta da wadanda lamarin ya shafa das u dauki mati kan wannan lamari na rashin tsauro musamman kan wadanda ke son kawo t=yamutsi da rikici a tsakanin mabiya mashabobin biyu manya na addinin musulunci wato shi'a da sunna a irakin.
1023049