Bangaren siyasa da zamantakewa: a daidai lokaci guda na juyayin rasuwar Imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran an shirya wata tattauanwa da fahimtar juna da kuma karawa juna sani kan Imam Ali (AS) wanda aka haifa a Ka'aba dakuma shi imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran ® wanda ya raya addinin musulunci ta hanyar assasa wannan jamhuriyar musulunci a Iran kuma kimanin malamai dari uku da dalibai day an jami'a za suka kasance wajan wannan taron.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi alkur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a daidai lokaci guda na juyayin rasuwar Imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran an shirya wata tattauanwa da fahimtar juna da kuma karawa juna sani kan Imam Ali (AS) wanda aka haifa a Ka'aba dakuma shi imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran ® wanda ya raya addinin musulunci ta hanyar assasa wannan jamhuriyar musulunci a Iran kuma kimanin malamai dari uku da dalibai day an jami'a za suka kasance wajan wannan taron.Da farkon wannan zaman taro da cibiyar al'adu ta babban masallacin imam Zaman (AJ) ta shirya babban dakin taro na masallacin Imam zaman (AJ ) a yankin Dasht barci na birnin Kabul Abdul Ali amini daya daga cikin malamai a hauzar ilimi ta birnin na kabul ya yi nuni da fitaccen hadisin nan da ke bayani kan ayyana imam Ali (AS) a matsayinsa na amirul mumunina (AS) da cewa; Khomeini a matsayinsa na wanda ya fito daga zurriyar wannan bawon Ali (AS) ya sadaukar da raid a rayuwarsa wajan sake raya wannan addini na musulunci a daidai lokacin da yake fuskantar matsaloli a ciki da wajen kasashen musulmi da kuma musulmin kansu. Mahalarta wannan taro dai sun yi bayani dalla dalla ta bangarori daban daban da suka shafi wadannan waliyai guda biyu da matsayinsu a tsakanin musulmi da wadanda ba musulminsa da kuma irin gudummuwar da suka bayar wajan ciyar da addinin musulunci a gaba.
1023790