IQNA

Za A Gudanar Da Taron Shekara Shekara Da Musulmin Kudu Maso Yammacin Faransa Ke Yi

Bangaren kasa da kasa: a ranar ashirin da bakwai ga watan khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a garin Tuluz musulmin kasar Faransa za su fara ganarwarsu ta farko da suke yiduk shekara kuma a bama musulmin kudu maso yammacin Faransa za su yi irin wannan ganawa.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi alkur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin da bakwai ga watan khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a garin Tuluz musulmin kasar Faransa za su fara ganarwarsu ta farko da suke yiduk shekara kuma a bama musulmin kudu maso yammacin Faransa za su yi irin wannan ganawa.An nakalto daga majiyar labarai ta pageshalal cewa; a wannan shekara ma kamar sauran shekarun da suka gabata musulmin kudu maso yammacin faransa za su yi ganawa da taron da suka yi shekara shekara da aka bas hi taken bana hadin kai wajibi ne ga musulmi kuma za a samu wakilcin kungiyoyi da cibiyoyi da hukumomi na musulmi na kasashen Suise da Beljuim da kuma mai masabkin baki Kasar Faransa. Da safiyar ranar ta ashirin da bakwai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya da misalign karfe tara da rabi na safiya agogon kasar ta Faransa za a fara wannan taro inda kungiyoyi na musulmi da kuma musulmi mahalarta taron za su saurari jawabai da dama kana bin da za a tattauanawa a wannan karo a wannan taro da kuma ya shafi muhimmanci da zama wajibi musulmi su hada kansu.
1024103