IQNA

Kungiyar Amal Ta Yi Kakusar Suka Dangane Da Shigar shugalar Kasashen Ketare A rikicin Kasar

15:55 - June 07, 2012
Lambar Labari: 2341671
Bnagaren kasa da kasa, kungiyar gwagwrmaya ta Amal a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka dangane da shigar shigula da kasahen ketare ke yi cikin abubuwan da suke faruwa a kasar sakamakon rikicin da yake faruwa ahalin yanzu haka a kasar Syria wanda kasashen yammacin turai da karnukan farautarsu daga larabawa suka haddasa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, kungiyar gwagwrmaya ta Amal a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka dangane da shigar shigula da kasahen ketare ke yi cikin abubuwan da suke faruwa a kasar sakamakon rikicin da yake faruwa ahalin yanzu haka a kasar Syria wanda kasashen yammacin turai da karnukan farautarsu daga larabawa suka haddasa domin cimma manufofinsu an siyasa.
Gwamnatin Syria ta bayyana dalilanta na korar wasu daga cikin jakadu da jami’an diplomasiyyar wasu daga cikin kasashen yammacin turai daga kasarta, da cewa hakan martini kana bin da suka aikata ga jakadunta da ke kasashensu a makon da ya gabata.
A zanatawar da yay i da manema labarai a birnin Damascus mataimakin ministan harkokin wajen kasar Syria Dr. Faisal Mikdad ya bayyana cewa, tun bayan da wasu daga cikin kasashen turai suka kori jakadun Syria daga kasashensu a makon da ya gabata, Syria ta bas u dama har ta mako guda domin ko sun yi tunani su gyara kuren da suka yi na diplomasiyya, ya ce bisa la’akari da cewa ba a shirye suke su gane korensu ba balantana su gyara, wannan ya sanya gwamnatin Syria ta mayar musu da martini daidai abin da suka yi.
A jiya ne gwamnatin Syria ta sanar da korar jakadun kasashen turai 17 da suka kori na jakadun makon da ya gabata bisa hujjar kisan gillar da aka yi mutane kimanin 100 a garin Haula, duk kuwa da cewa sun dauki matakin ne ba tare da an gudanar da bincike ba domin sanin wanda ya aikata hakan, wanda kuma al’ummar garin na Haoula dora alhakin wannan kisan gillada aka yi musu da ‘ya’yansu a kan ‘yan ta’adda, wadanda gwamnatin Syria ta ce kasashen turan ne da kansu suka kafa kuma suke ba su makamai da kudade.

1023857
captcha