IQNA

Fadakar Musulmi Na Da Babban Tasiri A Cikin Siyasar Yankin Gabas Ta Tsakiya

Bangaren al’adu da fasaha, fadakar musulmi da ake gani a halin yanzu tana babban tasiri a cikin sauyin harkokin suyasa ayankin gabas ta sakiya wanda da sannu hakan zai kawo karshen mamaya da kasashen ketare ke yi a cikin harkokin yankin tsawon shekaru.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa fadakar musulmi da ake gani a halin yanzu tana babban tasiri a cikin sauyin harkokin suyasa ayankin gabas ta sakiya wanda da sannu hakan zai kawo karshen mamaya da kasashen ketare ke yi a cikin harkokin yankin tsawon shekaru da suka shude.
Daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su ba tare da laifin tsaye ko na zaune ba.
Matasan sun taru ne a wani babban dandali da ke tsakiyar birnin Moscow na kasar Rasha inda suka daga tutoci na kasashen Rasha da kuma palastinedomin nuna cikakken goyon bayansu ga wannan al’umma da take fuskantar zalunci daga yahudawan sahyuniya, tare da amincewa manyan kasashe na duniya kama su Amurka da Birtaniya gami da Faransa da sauransu.
Wadannan daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su da yin kisan gilla a kansu.
1023798