IQNA

Marigayi Imam Khomeini (RA) Ya Bayar Da Gudunmawa Wajen Bunkasa Al’adun Addini

Bnagaren fikira da ilimi, marigayi Imam Khomeni (RA) ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa harkoki na ilmi da al’adun muslunci a cikin kasashen musulmi wanda hakan ke tabbatar da cewa juyin juya halin da ya jagoranta na dukaknin musulmi ne.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, marigayi Imam Khomeni (RA) ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa harkoki na ilmi da al’adun muslunci a cikin kasashen musulmi wanda hakan ke tabbatar da cewa juyin juya halin da ya jagoranta na dukaknin musulmi ne, bai kebantu da jamhuriyar muslunci ta Iran ba.
Daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na bababr cibiyar kula da harkokin musulunci cewa ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni da muke ciki.
A yayin wannan taro za a gabatar da jawabai wanda malamai da kuma masana gami da malaman jami’oi da maruta za su gabatar, inda za a yi bayani kan matsayinsa na ilimi da kuma irin gwagwarmayar da ya yi da manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, wadanda suke danne sauran al’ummomin duniya tare da dora manufofin siyasarsu kan duniya bisa zalunci.
Yanzu haka dai ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni na dubu biyu.
1023975