Bnagaren kasa da kasa, magajin garin birnin Niece a kasar Faransa ya sanar cewa za a mayar da wani babban masallaci mallakin mabiya addinin muslunci da ke birnin ya zama babbar tashar ‘yan sanda na wurin saboda masu kokawa da cewa sallar jam’i da musulmi suke gudanarwa na damunsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na leral cewa magajin garin birnin Niece a kasar Faransa ya sanar cewa za a mayar da wani babban masallaci mallakin mabiya addinin muslunci da ke birnin ya zama babbar tashar ‘yan sanda na wurin saboda masu kokawa da cewa sallar jam’i da musulmi suke gudanarwa na damunsu saboda haka suke karfafa mayar da shi ofishin jami’an tsaro.
Majalisar mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
Shigar da kara kan mutanen da suke nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai, yin hakan zai zama tamkar wani hannunka mai sanda ga sauran masu irin wannan akida asauran kasashen turai.
1025032