Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa dubban mutane ne suka gudanar da wani gangami a babban dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar domin kara nuna rashin amincewarsu da duk wani salo na dawo mulkin Husni Mubarak ta hanayar dawo da mukarrabansa da suka hada da Ahmad Shafiq.
A wani labarin kuma an gudanar da zaman shari’a a kotu kan kisan jama’a da ake zargin tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak da aikatawa a lokacin mulkinsa musamman a lokacin da mutanen kasar suke jerin gwanon hambarar da shi daga kan mulki shekarar ta gabata.
A wani labarin kuma karon farko za a fitar da jaridar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa wadda kuma za ta fara fito nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran jam’iyyar Gadir ta kasar Masar kumababban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar masar Muhammad Duraini shi ne ya bijiro da batun bude wannan jaridar, kuma zai bayar da gagarumar gudunmawarsa domin ci gabanta.
Wannan dai shi ne karon farko da za a fitar da wata jarida ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa a kasar.
1024994