Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na investir cewa, jagoran kungiyar Nahda a kasar Tunisia Rashid Ganushi ya bayyana cewa zai safka daga shugabancin kungiyar domin mayar da hankali kan lamurra na zamantakewa maimakon shagaltuwa da siyasa bayan kawar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ta Tunisia.
An gudanbar da zaman taro kan matsayin abubuwan da suke faruwa yanzu haka a kasashen musulmi da na larabawa a Kaduna da kuma tasirin haka a cikin al’ummar da kuma yadda zai bayar da damar mikewa domin fuskantar kalu bale daga siyasar danniya da cutar da musulmi.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa wasu daga cikin masana da kuma malamai sun kafa wata jam’iyar masu kishin islama a kasar Libya wanda shi ne karon farko da hakan ta kasance wadda ta kwashe shekaru arba’in da biyu karakshin mulkin kama karya na tsohon mulkin kama karya mu’ammar Gaddafi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan jam’iya tan ada manufofi na siyasa da suka yi daidai da mahnarta, ta yadda take son saka addini ya zama shi ne ma’anu a cikin dukaknin lamurranta na siyasa, haka nan kuma idan ta samu karbuwa a wajen al’ummar kasar tana sa ran za ta kawo gagarumin canji.
‘Yan siyasa da wasu daga cikin masana da kuma malamai sun kafa wata jam’iyar masu kishin islama a kasar Libya wanda shi ne karon farko da hakan ta kasance wadda ta kwashe shekaru arba’in da biyu karakshin mulkin kama karya na tsohon jagoran.
1025041