Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Barata cewa, ayyid Sadruddini Qobanchi babban limamin masallacin birnin Najaf ya bayayan cewa masu dauke da akidar kafirta sauran musulmi ne suke da alhakin kai harin ta’addanci kan bababn ginin wakafin shi’a da ke tsakiyar birnin Bagadaza a cikin makon da ya gabata da nufin haddasa rikici tsakanin musulmi, wanda kuma hakan bai yi nasara ba.
A bangare guda kuma kan batun na ‘yan ta’adda, tun bayan da gwamnatin kasar Syria ta sanar da fara yin aiki da shawarwarin mai shiga tsakani a rikicin a ranar 12 ga watan Afirilun da ya gabata, tun daga lokacin ne kasashen da suke mara baya ga ‘yan tawayen kasar a bayyane da kuma na boye suka sha alwashin kara yawan makaman da suke ba su da kuma makudan kudade, da nufin gaggauta kawo karshen mulkin shugaba Asad ko ta wace hanya.
Jaridar Le figaru ta kasar faransa ta bayar da wani rahoton sirri da ke cewa, sojojin kundunbala na Amurka (marines) suna horar da daruruwan ‘yan ta’adda a wani sansanin soji da ke kasar Jordan, tare da taimakon kasashen Qatar da Saudiyya, kuma ana tura wadanda suka samu horon ne zuwa kasar Syria domin kai hare-hare.
Jaridar ta ce abin ban mamaki shi ne, akasarin mutanen da ake baiwa horon sun fito ne daga kasashen larabawa 12 da kuma Pakistan, amma kuma suna shiga cikin Syria da sunan cewa su ‘yan adawar kasar ne da suke yaki da gwamnati, kuma wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Kofi Annan ya fara gudanar da aikinsa na kokarin sasanta bangarorin rikicin kasar ta Syria, duk kuwa da cewa kasashen da suke horar da ‘yan ta’adda da kuma daukar nauyin dukaknin ayyukan da suke yi cikin kasar Syria, su ne kan gaba wajen nuna cewa suna ma duniya suna goyon bayan shirin na Annan, wanda a lokaci guda a bayyane ba a boye ba su ne kuma suke rusa shirin nasa ta hanyar yunkurin daidaita kasar da neman haddasa yakin basasa.
1025664