IQNA

Amurka Da Yahudawa Su Ne Bayan Duk Wata Fitina A Kasashen Musulmi

20:49 - June 10, 2012
Lambar Labari: 2343797
Bangaren kasa da kasa, shugaban banagren harkokin sharia na kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta Hizbullah ya bayyana cewa Amurka da yahudawan sahyuniya su ne ke da hannu a cikin dukaknin matsaloli da fitunu a cikin kasashen musulmi a wannan zamani.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-lam cewa, sheikh Yabak shugaban banagren harkokin sharia na kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta Hizbullah ya bayyana cewa Amurka da yahudawan sahyuniya su ne ke da hannu a cikin dukaknin matsaloli da fitunu a cikin kasashen musulmi a wannan zamani da muke raywa.
A nata bangaren kasar Rasha ta bayyana damuwarta da yadda ayyukan da'addanci da kisan kiyashi ke kara yawaita a kasar Syria, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ne ya bayyana haka a yau asabar kuma ya kara da cewa kasar Rasha bazata amince da amfani da karfin soje a kan gwamnatin Syria a komitin tsaro na MDD ba.

Har'ila yau Lavrov ya kara da cewa kasar Rasha tana tunanin gudanar da taron kasa da kasa don tattaunawa matsalar kasar ta Syria nan gaba, kasar Rasha ta bayyana haka ne a dai dai lokacinda kasashen yamma suke kiraye kiraye na a hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-asad na kasar ta Syria.

A na shi bangaren shugaban kasar rasha Vledimir Putin ya bayyana rashin amincewarsa da duk wani kokari na canza gwamnati a kasar Syria, Putin ya fadawa shugaban kasar faransa Fransoa Holanda a wata haduwarsu a ranar 1 ga watan yuni da muke ciki cewa, yakamata a bi hanyar da ta dace don warware rikicin kasar na Syria.

A halin yanzu dai tawagar MDD masu sanya ido a kan bukatu gida 6 wanda kofi Anan ya gabatar na samar da zaman lafiya a kasar Syria tana ci gaba da sanya ido, amma yan tawaye masu samun makamai daga wasu kasashen larabawa da kawayensu na Turai basu taba dakatar da bude wuta ba tun bayan sojojin kasar Syria suka patattakesu a yankin hums.

1025363


captcha