Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masu bin diddigin lamurran siyasar kasashen musulmi da gabasd ta tsakiya sun imanin cewa boren kasashen larabawa da ya fara daga klasar Tunisia zuwa Masar har zuwa Libya yana fuskantar gagarumar matsala sakamakon rashin kalma guda da ke hada ra’ayoyin mutane kan sauyi musamman ma a cikin kwanakin da akesheda rikicin siyasa a wasu kasashen inda Libya ta zama babban misali kan hakan inda yan tawaye da ke dauke da makamai suke ta kashe kansu.
Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a rana ta biyu ta ci gaba da gwabza fada tsakanin wasu da aka ce masu mara wa gwamnatin Tripoli baya ne da kuma mayakan sa-kai 'yan kabilar Tubawa da ke kudancin kasar Libya ya kai mutane 23, yayin da wasu mutanen masu tarin yawan suka samu munanan raunuka.
Wani likita a garin Kufra inda aka yi wannan batakashi Dakta Taher Wahli, ya shaida wa manema labarai cewa akalla 'yan Kabilar Tubawa 20 ne cikinsu kuwa har da mata da kananan yara aka ajiye gawarwakinsu a asibitin da yake aiki, yayin da wasu mutanen fiye da 50 ke ci gaba da jinya a asibitin sakamakon harbinsu da aka yi da bindiga.
Shi kuwa shugaban kabilar ta Tubawa a garin Kufra Isa Abdulmajid, ya ce yawan Tubawan da sojoji masu biyayya ga Tripoli suka kashe daga jiya zuwa yau sun kai 28, inda ya ce abin da ke faruwa wani yunkuri ne na kawar da kabilarsa daga doron kasa. Wannan dai ba shi ne karo na farko da magoya bayan gwamnatin rikon kwarya ta Trioli ke kai hari a kan kabilar ta Tubawa ba, domin kuwa ko a cikin 'yan makwannin da suka gabata an samu barkewar irin wannan rikici tsakanin bangarorin biyu tare kuma da haddasa mutuwar mutane masu tarin yawa.
1025694