Bangaren fikira da limi, a zaman da ya gudana a birnin Pinjab an yi dubi kan sirar manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma ahlul baiti amincin Allah ya tabbata a gare su da nufin daukar darussa daga sirarsu mai albarka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shfin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa agabacin nahiyar Asia cewa a zaman da ya gudana a birnin Pinjab, an yi dubi kan sirar manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma ahlul baiti amincin Allah ya tabbata a gare su da nufin daukar darussa daga sirarsu mai albarka da kuma yadda musulmi za su yi koyi da hakan.
An bude wani masallaci a cikin bababr hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Bankok fadar mulkin kasar Thailand a wani mataki na kara tabbatar da mabiya addnin muslunci da ke kasar a matsayin daya daga cikin mabiya addinai sannu a kasar wadda akasarin mabiya addinain buda.
A wani bayani kuma shugaban kasar faransa gidan talabijin din kasar Faransa a zantawar da ta hada shi da gidan talabijin shugaban kasar ya bayyana cewa ba su lalae marhabin da Yusuf Qardawi bisa zarginsa da tunzura mutane wajen aikata ayyukan ta’addanci da kuma tsatsauran ra’yi, wanda a cewarsa Faransa ba ta amince da hakan ba.
Shugaban kasar ta Faransa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wata zantawa tare da sarkin kasar Qatar wanda daya ne daga cikin amintattu ga kasar Faransa, kuma shi ne wanda ya ajiye Qardawi a kasar bayan mahukuntan Masar sun kore shi sakamakon matakan da yake dauka na tunzura mutane zuwa tsatsauran ra’ayi, wanda kuma hakan ya kawo rashin jituwa tsakanin Qatar da Masar.
1026390