IQNA

Iran Ta Taka Gagarumar Rawa A Fadakar Al’ummar Yankin Gabas Ta Tsakiya

17:17 - June 11, 2012
Lambar Labari: 2344472
Bangaren siyasa da zamantakewa, jamhuriyar musulmunci ta Iran ta taka gagarumar rawa wajen al’ummar yankin gabas ta tsakiya kamar dai yadda duniya take shedawa a bubuwan da suke faruwa a halin yanzu a yankin duk kuwa da hankoron kasashen yammacin turai da karnukan farautarsu na yankin wajen ganin sun mayar da abun yadda suke so.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a taron tunmawa da marigayi Imam Khomeini (RA) da aka yi Tehran wasu mahalarta taron sun yi ishara da cewa, hakika jamhuriyar musulmunci ta Iran ta taka gagarumar rawa wajen al’ummar yankin gabas ta tsakiya kamar dai yadda duniya take shedawa a bubuwan da suke faruwa a halin yanzu a yankin duk kuwa da hankoron kasashen yammacin turai da karnukan farautarsu na yankin wajen ganin sun mayar da abun yadda suke so, ko kuma daidai da siyasarsu.
A cana Masar kuwa daruruwan ‘yan siyasa da masu kare hakkokin bil a dama a kasar sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsawa takarar da tsohon pira minitsn kasar karkashin shugabancin Mubarak Ahmad Shafiq tare da yin kira da a kawo karshen yunkurin dawo da mulkin kama karya da aka tumbuke.
Sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allha akasar Masar kuma shugaban jamiyar Algadir Muhammad Al-duraini ya bayyana cewa wajibi ne dukaknin bangarorin al’ummar Masar su shiga cikin batun tsara kundin tsarin mulkin kasar ta yadda hakkin wani bangare daga cikin al’ummar kasar ba zai bata ba.
Muhammad Al-duraini ya kirayi shugaban majalisar sojin kasar da ke mulki da kuma shugaban majalisar dokokin kasar,gami da pitra ministan gwamnatin wucin gadi jamal Ganzuri, da su kirayi dukaknin bangarorin siyasa da ma masu wakiltar wasu al’ummomi a kasar a lokacin kafa kwamitin tsara kundin tsarin muslkin kasar wanda za a nan gaba.
1026394



captcha