IQNA

Musulunci Na Kara Samun karbuwa a Cikin kasashen Yammacin Turai

20:32 - June 11, 2012
Lambar Labari: 2344587
Bangaren kasa da kasa, sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a ya yi nuni da cewa mutane da dama da suka hada da maza da mata a cikin kasashen yammacin turai suna karbar addinin musulunci fiye da sauran lokutan da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Ilslam cewa, sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a ya yi nuni da cewa mutane da dama da suka hada da maza da mata a cikin kasashen yammacin turai suna karbar addinin musulunci fiye da sauran lokutan da suka gabata duk kuwa da irin tsananin gabar da ake nuna ma musulmi.
Ana shirin gudanar da babban taro dangane da makomar fadakar musulmi a kasashen larabawa da kuma yadda hakan zai yi tasiri wajen dawo da karamar al’ummomin da suka samu kubuta daga zaluncin sarakuna da shugabanni masu danne hakkokin al’ummomin kasashensu.
Jam’iyyar Ikhwan ta kasar Masar ta tsayar da sakatarenta a mtsayin dan takarar neman shugabancin majalisar dokokin kasar tsakanin ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyarsu da adla wal hurriyya.
Gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu na Lebanon da Libya.
1015322
captcha