IQNA

Akwai Larurar Koyar Da yayanmu Kur'ani Da Tabiyar Ta Kur'ani

12:22 - June 12, 2012
Lambar Labari: 2345101
Bangaren kasa da kasa; Iyali da kuma cibiyoyi na koyar da kur'ani mai girma abubuwa biyu ne masu muhimmanci na koyar da yayanmu ilimin da sanin Allah tabaraka wata'ala kuma dole mu isar da wannan nauyi mai muhimmanci kamar yadda ya kamata da kuma zai taimaka wajan cimma burin da aka sanya a gaba.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: Iyali da kuma cibiyoyi na koyar da kur'ani mai girma abubuwa biyu ne masu muhimmanci na koyar da yayanmu ilimin da sanin Allah tabaraka wata'ala kuma dole mu isar da wannan nauyi mai muhimmanci kamar yadda ya kamata da kuma zai taimaka wajan cimma burin da aka sanya a gaba.Sheikh Abu Ihsan Albasri Alhamdani mai sanya ido kan zangon koyar da karatun kur'ani mai girma da ke karkashin hubbarin Imam Huseini (AS) kuma masani kan harkokin da suka shafi kur'ani a kasar Iraki kuma daya daga cikin mahardata kur'ani mai girma a wannan kasa a wata tattaunawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma ya yi bayanai kan wannan lamari da kuma Karin cewa;tushen koyar da kur'ani ga yara yana samo asali ne daga uawayen yaro da koyarwarsu da kuma himmar da suke da ita ta ganin yayansu sun yi hardar kur'ani mai girma kuma ta hanyoyi da dama kuma iri iri suna iya isar da wannan buri kamar salla azumi da fitar da zakka.
1026858
captcha