Bangaren kasa da kasa; bangaren alka'ida da ke kasar Iraki a ranar ashirin da daya ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wata sanarwa da acikinta ta ke daukan nauyi da alhakin kai harin bom da wasu abubuwa masu fashewa da aka tarwatsa a cibiyar yan shi'a a kasar Iraki mummunan harin rashin tausayi da imani da aka kai day a yi sanadiyar shahadar sama da mutane dari daya da talatin da shidda da kuma wasub daruruwa da suka samu raunuka.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: bangaren alka'ida da ke kasar Iraki a ranar ashirin da daya ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wata sanarwa da acikinta ta ke daukan nauyi da alhakin kai harin bom da wasu abubuwa masu fashewa da aka tarwatsa a cibiyar yan shi'a a kasar Iraki mummunan harin rashin tausayi da imani da aka kai day a yi sanadiyar shahadar sama da mutane dari daya da talatin da shidda da kuma wasub daruruwa da suka samu raunuka. Wannan mummunan hari na nuna rashin tausayi da imani da aka kai kan fararen hula dab a su san hawa balantana sabka bay a sa mutane da daman gaske na yin Allah wadai da tofin Allah tsine musamman idan aka yi la'akari cewa an kais hi ne a daidai lokacin da kungiyoyi da kasashe na musulmi da kungiyoyo da hukumomi da kuma daidaikum musulmi ke tashi fadin ganin an hada kai a tsakanin musulmi da kawo sulhu da kwanciyar hankali da tsaro a tsakanin musulmin.
1027218