Bangaren siyasa da zamantakewa, gagarumin ci gaba n da jamhuriyar musulunci ta Iran ta samu a cikin kankanin lokaci yana da dangantaka ne da irin kumajin da matasan kasar suke yi ne domin taimakon kasarsu da ganin ta ci gaba adukkanin bangarori na ilimi da kere-keren zaman da sauransu.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gagarumin ci gaba n da jamhuriyar musulunci ta Iran ta samu a cikin kankanin lokaci yana da dangantaka ne da irin kumajin da matasan kasar suke yi ne domin taimakon kasarsu da ganin ta ci gaba adukkanin bangarori na ilimi da kere-keren zaman da sauransu kamar yadda kowa ya shed a halin yanzu.
Shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar irin sauye-sauyen da ke faruwa a duniya wani lamari ne da ke nuni da cewa duniya ta kama hanyar tabbatuwar tsarin adalci.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Fonix ta kasar China inda ya ce tsarin da ke mulki a duniya a halin yanzu tsari ne da ke cike da zalunci da babakere kuma shi ne ummul aba'isin din irin koma bayan da al'ummomin duniya suke fuskanta da kuma hana su hakkokinsu. Don haka ne ma shugaban na Iran ya ce al'ummomi za su tabbatar da wadannan hakkoki na su ne kawai matukar suka ci gaba da yunkuri da kokari wajen dawo da su.
Yayin da aka tambaye shi kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar, shugaban na Iran cewa ya yi matsayar kasar Iran kan wannan lamarin dai a fili yake, dukkanin ayyukan nukiliyan Iran yana karkashin sanya idon hukumkar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Shugaban ya ce matsala guda cikin wannan lamari shi ne yadda manyan kasashen duniya suka shigo da siyasa cikin lamarin.
1027468