Kamfanin dillancin labaran iqn ay ahabarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a halin yanzu al’ummar kasar Masar na kokarin ganin bas u koma ga ‘yar gidan jiya ba a zaben shugaban kasa da za su gudanar nan da makonni masu zuwa inda za a kara tsakanin yan takara biyu wato tsohon pira ministan kasar Ahmad shafiq da kuma na bangaren kungiyar yan uwa musulmi.
Duk da cewa a wannan karo Nouri Al-Abbar ya ce an dage gudanar da zaben ne sakamakon rashin kammala aikin tantance masu jefa kuri'a, to amma a cikin kwanakin da suka gabata ya taba cewa tuni hukumarsa ta yi wa mutanen kasar milyan 2 da dubu 700 wannan rejista, wato fiye da 80% na wadanda ya kamata a yi wa rejistar, inda kuma ya ce ba makawa za a gudanar da zaben kafin ranar 19 ga wannan wata na yuni.
Karkashin dokokin sabuwar kasar ta Libya dai, wannan sabuwar Majalisa da za a zaba tana da wakilai 200 ne da za su fito daga bangarori daban daban na kasar, sannan kuma babban aikin Majalisar shi ne rubuta wa Libya sabon kudin tsarin mulki wanda zai fayyace karfin ikon sabon shugaban kasa da kuma sabuwar Majalisar dokokin da za a zaba a nan gaba da kuma karfin ikon kowanne daga cikinsu.
Daga cikin wakilai 200 da za su gudanar da wannan gagarumin aiki, kujeru 120 an ware su ne ga 'yan takara masu zaman kansu, yayin da sauran kujeru 80 aka ware wa sabbin jam'iyyun siyasar kasar domin yin takara a kai. A cewar hukumar zaben ta Libya, mutane fiye da dubu 4 ne suka gabatar mata da takardunsu na takarar wadannan mukamai, to sai dai a karkashin dokar zabe ta kasar da shugaban gwamnatin rikon kwarya Mustafa Abduljalil ya sanya wa hannu a cikin watan Janairun da ya gabata, duk wanda ya taba rike wani mukamin gwamnati a lokacin mulkin Kaddafi, ko wanda ya riki wani mukami a kwamitin juyin juya hali tun daga matakin uguwa har zuwa mataki na kasa a lokacin mulkin na kanar Kaddafi, to irin wadannan mutane an haramta masu tsayawa takara a wannan zabe da kuma sauran zabuka da za su biyo baya. 1027279