IQNA

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Ta Iran Ta Kirayi Wakilin Saudiyya A kasar

18:04 - June 13, 2012
Lambar Labari: 2346254
Bangaren siyasa da zamantakewa, bayan samun labarin kashe wasu iraniya da mahukuntan kasar Saudiyya suka ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi mutumin da ke kula da ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Tehran domin jin karin bayani kan hakan tare da ba shi sako ga kasar da yake wakilta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama na ma’aikatar harkokin wajen Iran cewa, bayan samun labarin kashe wasu iraniya da mahukuntan kasar Saudiyya suka ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi mutumin da ke kula da ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Tehran domin jin karin bayani kan hakan tare da ba shi sako ga kasar da yake wakilta tare da tabbatar da cewa idan dai har hakan ta tabbata to wannan mataki ne na rashin sanin diplomasiyya daga gwamnatin kasarsa.
A bangare guda kuma da dama daga cikin amsu bin diddigin lamurran siyasar kasar Masar suna hasashen cewa dan takarar kungiyar Ikhwanul musulmin ne zai lashe zaben shugaban kasar wanda aka fara gudanarwa a yau laraba kuma za a sanar da sakamakonsa na karshen bayan ‘yan kwanaki masu zuwa kamar dai yadda sakamakon jin ra’ayin jama’a ya nuna.
Bisa ga sakamakon jin ra’ayin dan takarar kungiyar Ikhwan shi ne zai lashe zaben da samun kuri’u masu rinjaye, daga shi kuma sai dan karar da ya ballae daga kungiyar, wanda kuma ya tsaya takarar ne a matsayin mai cin gishin kansa ba karkashin kungiya ba ko wata jam’iyya, to amma kuma bisa la’akari da cewa mutane suna zaben kungiya ne ko jam’iyya ba mutum bisa la’akari da shirinsa da kuma manufarsa ba, wannan ya sanya ake hasashen cewa ikhwan za su lashe.
Masu bin diddigin lamurran siyasar kasar Masar suna hasashen cewa dan takarar kungiyar Ikhwanul musulmin ne zai lashe zaben shugaban kasar wanda aka fara gudanarwa a yau laraba kuma za a sanar da sakamakonsa na karshen bayan ‘yan kwanaki, gami da wani dalilin da yake kara tabbatar da hakan wato sakamakon zaben waje da aka gdanar.
1028018

captcha