Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam cewa, a halin yanzu ana hada wani fim dangane da masallacin Qods mai alfarm ad akuma yadda yahudawan sahyuniya suka mamaye shi tun tsawon shekaru sama da sittin da suka gabata da kuma irin gallazawar da suka ma al’ummar palastinu mazauna yankin na asali.
Wani labarin kuma yana cewa sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin yin shirin fuskantar masu zanga-zangar lumana domin ranar kasa inda za su tuna da masallacin Quds ami alfarma da kuma yin kira da a kawo ma al’ummar palastine dauki daga zalunci da suke fama da shi da yahudawan sahyuniya da suka mamaye musu kasa da yankuna, a zirin gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan.
Bayanin ya ci gaba da cewa dubban daruruwan palaesyinawa v acikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma zirin Gaza suke cikin gudanar da zanga-zangar ranar kasa, domin nuna duniya cewa batun palastinu yana raye, a hankoron da wasu daga cikin munafukan kasashen larabawa suke yi na mayar da maganarsu a bun mantawa baki daya a cikin duniyar larabawa da ma duniya baki daya.
Yanzu haka sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin yin shirin fuskantar masu zanga-zangar lumana domin ranar kasa inda za su tuna da masallacin Qods ami alfarma da kuma yin kira da a kawo ma al’ummar palastine dauki daga zalunci da suke fama da shi da yahudawan sahyuniya masu tsananin zalunci kan dan dam.
1028455