IQNA

Fadakar Musulmi Na Da Dangantaka Kai Tsaye Da Makomar Yankin Gabas Ta Tsakiya

18:03 - June 13, 2012
Lambar Labari: 2346260
Bangaren kasa da kasa, fadakar da al’ummar musulmi suke samu a halin yanzu tana da dangantaka kai tsaye da makomar yankin gabas ta tsakiya a lokuta masu zuwa domin hakan ya samar da sauyin da babu wanda ya yi tsammanin zai kasance a cikin wannan lokaci a yankin baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, fadakar da al’ummar musulmi suke samu a halin yanzu tana da dangantaka kai tsaye da makomar yankin gabas ta tsakiya a lokuta masu zuwa domin hakan ya samar da sauyin da babu wanda ya yi tsammanin zai kasance a cikin wannan lokaci a yankin baki daya da kuma ya yi tasiri har zuwa wankuna na duniya.
Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabbi a yau dangae da abubuwan da suke faruwa yankin gabas ta tsakiya da kuma matsayin kungiyar a kansu musamman ma, wadanda suka danganci al’ummar larabawa da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila.
Rahoton ya ci gaba da cewa a cikin jawabin nasa Sayyid Hassan Nasrullah zai mayar da hankali kan muhimman abubuwan da suke a gaban larabawa a halin yanzu, musamman a lokacin da shugabanninsu da sarakunansu suka zama manyan ‘yan kore ga manufofin haramtacciyar kasar Isra’ila da babbar uwar shaidanu Amurka.
Haka nan kuma zai yi tsokaci kan zaman taron koli na shugabannin larabawa da aka gudanar a birnin Bagadaza na kasar Iraki, tare da halartar wasu daga cikin shugabannin kasashen larabawa, yayin da larabawa tekun fasha suka kaurace ma zaman taron ba tare da bayyana wani dalili ba.


1025931




captcha