Bangaren kasa da kasa, an bude tashar talabijin ta Almayadin a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon da nufin bayar da labarai na gaskiya kan abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya musamman abin da ya shafi palastinu da kuma boren kasashen kasashen larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na dp-news cewa, a jiya an bude tashar talabijin ta Almayadin a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon da nufin bayar da labarai na gaskiya kan abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya musamman abin da ya shafi palastinu da kuma boren kasashen kasashen larabawa sabain abin da wasu kafafen yada labarai masu bakaken manufofi suke yadawa.
Wannan tasha za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ne tare da sauran kafofin yada labarai na kasa da kasa da kuma na kasashen larabawa da suke gudanar da shirye-shiye kan tauraron dan adam da adadinsu ya kai 700, kamar yadda tashar, kamar a ka kawshe kimanin watanni tara a jere ana ta kokarin samar da wannan tasha domin gudanar da wannan gagarumin aiki.
Bude tashar talabijin ta Almayadin a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon da nufin bayar da labarai na gaskiya kan abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya musamman abin da ya shafi palastinu da kuma boren kasashen kasashen larabawa a halin, hakan wani bababn kalu bale ga sauran kafofin yada labarai masu juya gaskiyar labari domin ya yi daidai da siyasar yahudawan sahyuniya da kasashen yammacin turai. 1028202