Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin wakilan majalisar dokokin kasar Tunisia daga jam’iyyar masu kishin islam ta Nahdah ya bayyana cewa karuwar mutane masu tsattauran ra’ayi da wuce gona da irin akidar musulnci yana tattare da gagarumin hadi a cikin al’ummar musulmi kamr yadda duniya take sheda abin da ‘yan salafiya suke yi da sunan musulunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bussiness news cewa, Walid Bnnani daya daga cikin wakilan majalisar dokokin kasar Tunisia daga jam’iyyar masu kishin islam ta Nahdah ya bayyana cewa karuwar mutane masu tsattauran ra’ayi da wuce gona da irin akidar musulnci yana tattare da gagarumin hadi a cikin al’ummar musulmi kamr yadda duniya take sheda abin da ‘yan salafiya suke yi da sunan musulunci wanda kuma msuulunci ya yi hannaun riga da abin da suke yi.
Gwamnatin kasar Tunisia ta kafa dokar hana fita daga karfe 9 na dare zuwa 5 na safe a babban birnin kasar Tunis da kuma wasu wasu biranin kasar guda 7 don dakatar da tashe tashen hankulan da ke faruwa a wadannan bira ne tun kwanaki biyu da suka gabata, yansanda sun yi harbi a sama don tarwatsa masu zanga zanga don nuna fushinsu kan wani zane na batanci ga addinin musulunci da aka yi a wasu birarnin kasar.
Biranen da wannan dokan hana yawon ya shafi sun hada da Tunis bababan birnin kasar, da anguwanni na Ben Arus, Arina da kuma Manuba wadanda suke kusa da babban birnin kasar. Sai kuma biranen Sosse Monasti Jenduba da Ben Gudan, majiyan ma'aikatar cikin gida a birnin Tunis ta bayyana cewa ana tsare da mutane 90 kan rigingimun tun ranar lahadi da ta gabata.
1027991