Bangaren kasa da kasa, an kafa wata kungiya mai suna ikhwan mumunin a hijaz wadda za ta yi gwagwarmaya domin kawar da sarakunan Ali-saud da suke mulki a kasar Saudiyya tare da danne al’ummar kasar wadanda suke kokawa da yanayin da suke na siyasa da tattalin arziki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad ta kasar Lebanon cewa, an kafa wata kungiya mai suna ikhwan mumunin a hijaz wadda za ta yi gwagwarmaya domin kawar da sarakunan Ali-saud da suke mulki a kasar Saudiyya tare da danne al’ummar kasar wadanda suke kokawa da yanayin da suke na siyasa da tattalin arziki mafi muni fiye da dukkanin kasashen yankin tekun fasha.
Wannan kungiya dai ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta daidai da yanayi domin tabbatar da cewa al’ummar kasar saudiyya sun samu ‘yanci daga mulkin mulukiyya na gidan Ali-saud wadanda suka mayar da kasar da dukiyarta da duka bin da ta malalka da mutanen da ke cikinta amatsayin wani abu mallakinsu, da kuma suke juya shi yadda suka ga dama.
Kafa wannan kungiya mai suna ikhwan mumunin a hijaz wadda za ta yi gwagwarmaya domin kawar da sarakunan Ali-saud da suke mulki a kasar Saudiyya tare da danne al’ummar kasar wadanda suke kokawa da yanayin da suke na siyasa da tattalin arziki, wannani babban ci gaba ne amahangar masu bin diddigin lamurran siyasar yankin.
1029489