IQNA

Makomar Yankin Asia Dangane Da Fadakar Musulmi Da Ke Fadada A koina

20:29 - June 14, 2012
Lambar Labari: 2346735
Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar da zaman taro dangane da gagarumin ci gaba n da ake samu a kasashen nahiyar Asia tun bayan fara bore a cikin wasu kasashen larabawa wanda hakan ya jawo babbar fadaka ga musulmi inda suke neman hakkokinsu da aka haramta musu daga miyagun shugabanni da sarakuna.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da zaman taro dangane da gagarumin ci gaba n da ake samu a kasashen nahiyar Asia tun bayan fara bore a cikin wasu kasashen larabawa wanda hakan ya jawo babbar fadaka ga musulmi inda suke neman hakkokinsu da aka haramta musu daga miyagun shugabanni da sarakuna kamar yadda duniya take shedawa ayankin gabas ta tsakiya.
A wani taron manema labarai da ya gudanar da tare da takwaransa na Iran ministan harkokin wajen kasar Rasha ya zargi Amurka da kawayenta da hannu a aikewa da makamai ga 'yan tawayen kasar Siriya.
A taron manema labarai da ya gudanar da takwaransa na kasar Iran a ziyarar aikin da yake gudanarwa a kasar ta Iran a yau laraba; Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewar wasu kasashe suna kokarin shirya dabarar kunna wutar yaki a kasar Siriya kamar yadda aka yi a kasar Libiya.
Lavrov ya kuma yi kakkausar suka kan siyasar fuska biyu da wasu kasashe ke yi kan rikicin kasar Siriya, inda a fili suke bayyana wajabcin kawo karshe tashe tashen hankula a Siriya, sannan a ta karkashin kasa suna tura makamai ga 'yan tawayen kasar.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya yi nuni da irin matakan da 'yan ta'adda a Siriya suke dauka na kokarin ganin sun hana gwamnatin kasar aiwatar da gyare gyare a harkar tafiyar da kasar ta Siriya da ci gabanta. Salihi ya kuma jaddada matsayin kasar Iran na rashin amincewa da tsoma bakin kasashen waje a rikicin kasar ta Siriya.
1028952

captcha