IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki Da Kuma Harda Ta Kasa Baki Daya A Senegal

20:28 - June 14, 2012
Lambar Labari: 2346739
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Dakar na kasar Senegal da ke samun halartar daruruwan daliban kur’ani da suke gudanar da gasar a dukkanin bangarorinta na harda da kuma kir’a kamar dai yadda cibiyar shirya gasar kur’ani ta kasar ta sanar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Dakar na kasar Senegal da ke samun halartar daruruwan daliban kur’ani da suke gudanar da gasar a dukkanin bangarorinta na harda da kuma kir’a kamar dai yadda cibiyar shirya gasar kur’ani ta kasar ta sanar a jiya.
Wani rahoton na daban kuma yana cewa kasar Amurka tana kara fadada ayyukan leken asirinta a duk fadin nahiyar Afirka ta hanyar kananan sansanonin sojinta da suke nahiyar sannan kuma ta hanyar fakewa da batun fada da ta'addanci, jaridar Washington Post ta Amurkan ta bayyana cewar hukumar sojin Amurkan sun kirkiro wasu 'yan kananan sansanonin sojin sama a duk fadin Afirkan da kuma ba da horo ga wasu jami'an soji duk dai da nufin ci gaba da sanya ido da tattaro bayanan sirri kan kasashe daban-daban na nahiyar.
Jaridar ta ce Amurkan tana amfani da wasu 'yan kananan jiragen sama da ta ajiye su a irin wadannan sansani da sunan jirage ne na fararen hula, amma kuma an sanya musu na'urori da kyamarori masu karfin gaske da suke dauko hotuna da kuma duk wani motsi da kuma maganganun da ake yi ta wayar salula.
Wasu rahotanni sun ce wadannan sansanoni na sojin Amurkan dai suna nan ne a kasashe irin su Mauritaniya, Burkina Faso, Ethiopia, Djibouti, Uganda, Sudan ta Kudu, Kenya da sauransu, kamar yadda kuma rahoton ya ce sojojin Amurkan suna ci gaba da ba da horo ga sojojin wasu kasahsen Afirkan irin su Aljeria, Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritaniya, Morocco, Nijar, Nigeria, Senegal da Tunusia da sunan fada da ta'addanci.
1029120

captcha