IQNA

An Kafa Dokar Haramta Keta Alfarmar Abubuwan Da Ake Girmamawa A Addini A Tunisia

20:28 - June 14, 2012
Lambar Labari: 2346740
Bangaren kasa da kasa, an kafa wata doka a cikin kundin tsarin dokokin kasar Tunisia da ke haramta cin zarafin addini ko keta alfarmarsa kamar dai yadda dokar ta fara aiki daga lokacin amincewa da ita a babban zauren majalisar dokokin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar cewa, an kafa wata doka a cikin kundin tsarin dokokin kasar Tunisia da ke haramta cin zarafin addini ko keta alfarmarsa kamar dai yadda dokar ta fara aiki daga lokacin amincewa da ita a babban zauren majalisar dokokin kasar wadda akasarin mambobinta masu kishin islama ne da suka fito daga jam’iyyar Nahda.
A can Libya kuwa hukumar zaben kasar ta bakin shugabanta Nouri Al-Abbar, ta bayyana cewa sai a ranar 7 ga watan Yuli mai zuwa ne idan Allah ya kai mu za a gudanar da zaben Majalisar da za ta rubuta wa kasar sabon kundin tsarin mulki, kuma dage zaben ya samo asali ne daga wasu matsaloli masu nasaba da rashin kammala ayyukan tantance sunayen mutanen da suka cancanci jefa kuri'a a wannan zabe wanda shi ne na farko da za a gudanar a kasar da ke kokarin dora kanta a kan turbar dimokuradiyya bayan kawar da Kanar Mu'ammar Kaddafi daga karagar mulki.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake dage ranar gudanar da wannan zabe a kasar ta Libya ba, wanda kuma gudanar da shi zai iya kansacewa wani ma'auni da zai fayyace matsayin gwamnatin rikon kwaryar kasar wadda kasashen Turai da Amurka da kuma wasu kasashen Larabawa suka yi ruwa da tsaki wajen ganin cewa an kafa ta a daidai lokacin da tsohon shugaban kasar Kanar Kaddafi yake zaune daram a cikin fadarsa ta Babal Azaziyya da ke birnin Tripoli.
Duk da cewa a wannan karo Nouri Al-Abbar ya ce an dage gudanar da zaben ne sakamakon rashin kammala aikin tantance masu jefa kuri'a, to amma a cikin kwanakin da suka gabata ya taba cewa tuni hukumarsa ta yi wa mutanen kasar milyan 2 da dubu 700 wannan rejista, wato fiye da 80% na wadanda ya kamata a yi wa rejistar, inda kuma ya ce ba makawa za a gudanar da zaben kafin ranar 19 ga wannan wata na yuni.
Karkashin dokokin sabuwar kasar ta Libya dai, wannan sabuwar Majalisa da za a zaba tana da wakilai 200 ne da za su fito daga bangarori daban daban na kasar, sannan kuma babban aikin Majalisar shi ne rubuta wa Libya sabon kudin tsarin mulki wanda zai fayyace karfin ikon sabon shugaban kasa da kuma sabuwar Majalisar dokokin da za a zaba a nan gaba da kuma karfin ikon kowanne daga cikinsu. 1029014










captcha