Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-anawar ta kasar cewa, babban editan wannan jaridarida Adil Jaujari ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya na iyakacin kokarinta domin ganin ta watasa akidar wahabiyanci da kafirta a musulmi a duniya da nufin aiwatar da aikin da aka dora domin shi na kare manufofin kasashen yammacin turai da wargaza a ddinin musulunci wanda kuma wannan ita ce manufar yahudawan sahyuniya.
Da dama daga cikin malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an ya nakalto daga shafin sadrawa an yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu, sakamakon danne su da wahabiyan kasar ke yi.
1029019