IQNA

Za A Bude Wata Babbr Cibiya Ta Mabiya Tafarkin Iyalan Gidan Manzo A Lebanon

20:01 - June 16, 2012
Lambar Labari: 2347972
Bangarn kasa da kasa, ana shirin bude wata babbar cibiya ta ilimi da bunkasa al'adu ta ahlul bait (AS) a garin Babliya da ke kudancin kasar Lebanon tare da halartar wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar da kuma 'yan majalisa wadanda duk za su halarci bikin bude wannan cibiya a babbn gininta.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lebanonfiles cewa, ana shirin bude wata babbar cibiya ta ilimi da bunkasa al'adu ta ahlul bait (AS) a garin Babliya da ke kudancin kasar Lebanon tare da halartar wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar da kuma 'yan majalisa wadanda duk za su halarci bikin bude wannan cibiya a babbn gininta da yake a yankin.
Wani rahota ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana duba yiwuwar ta taimaka wa yan tawayen kasar Siriya masu yaki da gwamnatin Bashshar Asad ta hanyar ba su manyan makamai.
A jiya Jumaa ne jaridar The Daily Telegraph ta kasar Biritaniya ta buga labarin cewa masu dauke da makamai na kasar Siriyan sun yi tarurruka da manyan jamian gwamnatin Amurka kuma sunn bukaci a ba su manyan makamai da zasu hada da rokoki da zasu taimaka musu yakar gwamnatin Siriya.
Rahoton ya ce a makon da ya gabata wani jigo na kungiyar da ke dauke da makamai mai kiran kanta "Rundunar Siriya Mai Yanci" ya gana da jami'i na musamman mai kula da harkokin da suka shafi Gabas ta Tsakiya, a maaikatar harkokin wajen Amurka, yan siyasan kasar Amurka da dama sun bukaci a taimaka wa yan tawayen Siriya da makamai amma kasar Rasha ta yi kashedin cewa yan tawayen suna aikata ayyukan taaddanci a kasar Siriya.
1030374
captcha