Bangaren kasa da kasa, za a nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da dutse wanda shi ne irinsa na farko da aka taba bugawa kuma za anuna shi ne a cikin watan Ramadan mai zuwa kamar dai yadda bangaren kula da harkokin shirya baje koli na kur’ani ya sheda.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na CHTN cewa za a nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da dutse wanda shi ne irinsa na farko da aka taba bugawa kuma za anuna shi ne a cikin watan Ramadan mai zuwa kamar dai yadda bangaren kula da harkokin shirya baje koli na kur’ani ya sheda ga manema labarai.
Babban kwamitin shirya gasa ta karatun kur’ani da kuma harda a kasar hadaddiyar daular larabawa ya sanar cewa an kammala dukaknin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya kamar dai yadda aka saba gudanarwa a kasar a kowace shekara.
Bayanin ya ci gaba da cewa gudanar da irin wannan taro na gasar karatun kur’ani a kasar ta haddaiyar daular larabawa na daga cikin abubuwan da akan gudanar shekara-sheakara a garuruwa daban-daban na kasar, inda awannan karon za agudanar da wannan taron a garin Ra’asulkhaimah.
Babban kwamitin shirya gasa ta karatun kur’ani da kuma harda a kasar hadaddiyar daular larabawa ya sanar cewa an kammala dukaknin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya, da aka saba gudanarwa akasar hadaddiyar daular larabawa. 1030672