IQNA

Taron Tunawa Da Ranar Aiko Manzon Allah (SAW) A Kasar Rwanda

21:09 - June 19, 2012
Lambar Labari: 2350125
Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar da zaman taro na tunawa daranar aiko manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a birnin Bujumbura na kasar Rwanda tare da halartar masana da malaman addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da zaman taro na tunawa daranar aiko manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a birnin Bujumbura na kasar Rwanda tare da halartar masana da malaman addini lamarin da ke nuni da irin gagagrumin ci gaban da addinin muslunci ke samu a cikin klasashen Afirka.
malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mabiya addinai kamar majamioin mabiya addinin kirista.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
1032162


captcha