Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Masar suna ta muna bayan nasara da masu kishin islama suka samu a zabukan shugaban kasa da aka gudanar zagaye na biyu a kasar tsakanin dan takarar kungiyar yan uwa musulmi da kuma mai zaman kana kuma tsohon pira ministan tsohuwar gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mutanen kasar Masar suna ta muna bayan nasara da masu kishin islama suka samu a zabukan shugaban kasa da aka gudanar zagaye na biyu a kasar tsakanin dan takarar kungiyar yan uwa musulmi da kuma mai zaman kana kuma tsohon pira ministan tsohuwar gwamnatin kasar ta Masar.
Al'ummar Masar sun fito domin bayyana adawarsu kan abin da suka kira juyin mulki da Majalisar mulkin Soji kasar ta yi ga juyin juya halin da al'ummar kasar suka yi, a yau talata ne dubban jama'ar kasar Masar suka gudanar da zanga zanga a sassa daban daban na kasar tare da gudanar da taron gangami a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira domin bayyana rashin amincewarsu da matakin da Majalisar mulkin sojin kasar ta dauka na rusa zababbiyar Majalisar Dokokin Kasar da kuma sanarwar da ta fitar na rage karfin mulkin da shugaban kasa ke da shi.
Kungiyar gwagwarmaya ta shiga ga watan Aprilu da ta jagorancin kifar da tsohuwar gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak da kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Ihwan ne suka kira taron gangamin na yau, kuma sun lashi takwabin ci gaba da gudanar da gwagwarmaya har sai sun tilasta wa Majalisar mulkin sojin kasar komawa kan ingantaccen tsarin dimokaradiyya.
1032907