Bangaren al’adu da fasaha, an fara watsa shiri a tashar talabijin din diyanat a kasar Turkiya a matsayin gwaji a kowace rana wanda zai rika watsa shirin addini tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar kamar yadda bangaroribn da abin ya shafa uka sanar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an fara watsa shiri a tashar talabijin din diyanat a kasar Turkiya a matsayin gwaji a kowace rana wanda zai rika watsa shirin addini tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar kamar yadda bangaroribn da abin ya shafa uka sanar.
an nuna wasu daga cikin kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga a cikin harsunan duniya daban-daban da suke da alaka da yarukan da ake yin rubutu da su domin isa da ilmomi ga sauran mutane na sassan duniya da nufin kara isar da sakon da ke tatatre a cikin kur’ani mai tsarki.
yanzu haka an fara yin rijistar sunayen mutanen da suke bukatar gudanar da aikin hajjin bana birnin Lahour na kasar Pakistan wanda shirin yakegudana a halin yanzu babban husainiyar Minhaj da ke birnin kuma kofa bude take har yanzu mutanen da suke bukata tafiya ta wannan hanya a wannan shekara.
Kasar pakistan dai na daga cikin kasashen musulmi da suka fi yawan mabiya wanna addini, inda adadinsu ya kai sama da miliyan dari da saba’in, kuma suna samun gagarumin ci gaba da fuskar yada manufofi na addini ta hanyoyi da suka dace a zamannce kamar yadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar, wanda hakan ke tabbatar da ci gaban addini a yankin na kudancin nahiyar Asia. 1034041