Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka dai sojojin kasar Masar sun dana wa masu kishin islam tarko a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a kasar wanda yake tattare da rikici a cikinsa wanda kuma ake ganin cewa matukar dai ba su hattara ba to za a koma ga yar gidan jiya ne babu makawa domin kuwa sojin suna a ci gaba da zama karkashin mulki ne na kama karya irin na tsohon shugaban kasar.
Rahotonnin da suke fitowa daga yankin na Zirin Gaza suna bayyana cewa; a jiya laraba jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna ta shawagi a sararin samaniyar yankin Zirin Gaza da nufin murkushe duk wani yunkurin 'yan gwagwarmayar Palasdinawa na mai da martani kan hare haren zaluncin da suke fuskanta, kuma har ya zuwa yanzu babu labarin batun kulla wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Palasdinawa da haramtacciyar kasar ta Isra'ila.
A sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida da na tsaro da suke karkashin zababbiyar gwamnatin Palasdinawa da ke yankin Zirin Gaza suka fitar a jiya laraba; sun yi Allah wadai da hare haren zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan yankin Zirin Gaza ta sama da kasa, tare da jaddada cewar jami'an tsaron Palasdinawa da kungiyoyin gwagwarmaya a yankin zasu dauki matakan mai da martani kan wannan hare hare na wuce gona da iri da suke fuskanta.
Har ila yau sanarwar ta fayyace cewar manufar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na tsananta kai hare hare kan yankin Zirin Gaza a wannan lokaci ita ce; kara janyo rudani da rikici da zasu kara janyo tabarbarewan matakan tsaro a dukkanin yankin gabas ta tsakiya da kuma kokarin sake aiwatar da kisan kiyashi kan Palasdinawa kamar yadda ya faru a shekara ta 2008, don samun damar kara shimfida bakar siyasarsu ta zalunci da kwace a yankunan Palasdinawa.
A hare haren zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar kan yankin Zirin Gaza a cikin kwanaki 22 na karshen shekara ta 2008, Palasdinawa kimanin 1500 da suka hada da mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma suka jikkata tare da lalata duk wasu wajaje masu muhimmanci da suke yankin da nufin kara durkusar da Palasdinawa.
1032824