Bangaren kasa da kasa, makaranta kur’ani mai tsarki palastinawa sun taka gagarumar rawa a bangaren karatu a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar wanda hakan ke nuni da irin gagarumin ci gaban da aka samu a tsakanin palastinawa ta fuskacin raya kur’ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, makaranta kur’ani mai tsarki palastinawa sun taka gagarumar rawa a bangaren karatu a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar wanda hakan ke nuni da irin gagarumin ci gaban da aka samu a tsakanin palastinawa ta fuskacin raya kur’ani mai tsarki.
Rahotonnin da suke fitowa daga yankin na Zirin Gaza suna bayyana cewa; a jiya laraba jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna ta shawagi a sararin samaniyar yankin Zirin Gaza da nufin murkushe duk wani yunkurin 'yan gwagwarmayar Palasdinawa na mai da martani kan hare haren zaluncin da suke fuskanta, kuma har ya zuwa yanzu babu labarin batun kulla wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Palasdinawa da haramtacciyar kasar ta Isra'ila.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida da na tsaro da suke karkashin zababbiyar gwamnatin Palasdinawa da ke yankin Zirin Gaza suka fitar a jiya laraba; sun yi Allah wadai da hare haren zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan yankin Zirin Gaza ta sama da kasa, tare da jaddada cewar jami'an tsaron Palasdinawa da kungiyoyin gwagwarmaya a yankin zasu dauki matakan mai da martani kan wannan hare hare na wuce gona da iri da suke fuskanta.
Har ila yau sanarwar ta fayyace cewar manufar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na tsananta kai hare hare kan yankin Zirin Gaza a wannan lokaci ita ce; kara janyo rudani da rikici da zasu kara janyo tabarbarewan matakan tsaro a dukkanin yankin gabas ta tsakiya da kuma kokarin sake aiwatar da kisan kiyashi kan Palasdinawa kamar yadda ya faru a shekara ta 2008, don samun damar kara shimfida bakar siyasarsu ta zalunci da kwace a yankunan Palasdinawa.
1034621